Jummaʼa 23 Oktoba 2026 - 20:48
Raunin Amurka Guda Goma Sun Bayyana, Lokacin Haƙurin Dabarun Iran Ya Ƙare

Hauza/ Ayatullah Alireza A’arafi, limamin Juma’a a birnin Qum, ya bayyana cewa yaƙin baya-bayan nan ya fallasa raunin Amurka a fannoni daban-daban, yana mai jaddada cewa Iran za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare mutuncinta da martabarta.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewar a hudubar Juma’a da ya gabatar a Masallacin Quds da ke Qum, Ayatullah A'arafi ya ce Amurka da Isra’ila ne suka tilasta wa Iran da Ƙungiyoyin Gwagwarmaya yaƙi, amma ba su cim ma manufofinsu na durƙusar da Iran ba.

Ayatullah A’arafi ya bayyana raunin Amurka guda goma da suka haɗa da ƙaruwa da ƙiyayyar da duniya ke yi mata, raunin ƙarfin sojinta a yaƙin da ba a yin sa da daidaitaccen ƙarfin soji, raunin tattalin arzikinta, sabbin hanyoyin matsin lamba da Iran za ta iya amfani da su, rikice-rikicen cikin gida a Amurka da Isra’ila, da kuma bayyana zaluncin Amurka ga sauran al'ummomi.

Ya kuma jaddada cewa zamanin kai hari sannan a gudu ya ƙare, tare da bayyana cewa lokacin haƙurin dabarun Iran da la’akari da abubuwan da suka hana ta ɗaukar mataki ya wuce. Ya yi gargaɗin cewa duk wani sabon hari zai iya jawo wa maƙiya babbar illa.

Limamin ya yi kira ga jami’an Iran da su nuna ƙarfi a gaban maƙiya, su ƙarfafa shirye-shiryen tattalin arziki da na tsaro, sannan su tabbatar da haɗin kan al'umma da biyayya ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewar al'umma a tarukan jama'a da sallolin Juma'a.

Gargaɗi ga ƙasashen yankin

Ayatullah A’arafi ya yi kira ga gwamnatin Azarbaijan da ta dakatar da matakan da suka saɓa wa ƙa'idojin Musulunci, musamman waɗanda suka shafi hijabi. Haka kuma, ya buƙaci gwamnatocin Saudiyya da Bahrain su dakatar da ɗaurin malamai da matasa, tare da yin kira ga hukumomin diflomasiyya su taimaka wajen kuɓutar da waɗanda ake tsare da su.

Matsayin Sayyida Fatima Zahra (S.A.)

A hudubarsa ta farko, ya bayyana babban matsayin Sayyida Fatima Zahra (S.A.) a mahangar Shi'a da Ahlus-Sunna, yana mai cewa akwai abubuwa da dama da suka haɗa mazhabobin biyu game da falalolinta.

Ya ce Sayyida Fatima (S.A.) abin koyi ce ga mata da maza a fannonin ilimi, ibada, tarbiyya, hidimar al'umma, kare Wilaya da jagoranci a lokacin rikici.

Ya jaddada cewa hijabi da kamun kai ba abubuwa ne na zahiri kawai ba, suna daga cikin alamomin wayewar Musulunci. Ya kuma bayyana cewa rayuwar Sayyida Fatima (S.A.) tana nuna cewa mace za ta iya haɗa ilimi, aiki a cikin al'umma da tsarkin ruhi, ba tare da barin ƙa'idojin addininta ba.

A ƙarshe, ya yi nuni da ruwayoyin Shi'a da Ahlus-Sunna da suka bayyana matsayi mai girma da Sayyida Fatima Zahra (S.A.) za ta samu a ranar Alƙiyama.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha